JOLLOF DIN DASHISHI


_*Ingredients*_
_Alkama_
_Attarugu_
_Albasa_
_Maggi_
_Gishiri_
_Curry_
_Mai_
_Carrot_
_Cabbage_

_*METHOD*_
_Zaki gyara alkamar ki, ki wanke ta ki rege saboda tsakuwa ko qasa, zaki bada a 6arza maki ita, manya 6arji ko qanana duk dai wanda kikafi so, bayan an kawo maki saiki wanke wannan 6arjin alkaman naki saiki daura tukunya da madanbaci akan wuta, saiki zuba wannan alkamar taki acikin madanbacin ki rufe sosae yadda zata turaru sosae, zaki bata kamar 20mnts saiki sauke ki wanke, bayan kin wanke saiki dauko attarugunki wanda kin riga kin jajjaga shi tare da albasar da kika yanka saiki sanya acikin wannan dashishin naki da kika wanke, saiki sanya gishiri da duk kalar maggin da kikeso da curry saiki sanya carrot dinki wanki kin riga kin yanka shi tare da cabbage dinki saiki maida dashishin naki akan wuta bayan kin gama hada komai da komai saiki barshi ya cigaba da dahuwa ki bashi kamar 30mnts zuwa 40 don ya dahu sosae saiki sauke ki samu waje mai fadi sosae ki juyeshi aciki saiki sanya man gyada ki motsa sosae shikenan kin gama_😋😋😋

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SHINKAFA DA MIYAR TANKWA

SWEET ALALE

YADDA AKE WAINAR SEMOVITA