SWEET ALALE

SWEET ALALE*🥛🥛🍳🍳

*KAYAN HADI*

'Kwai
Madara

*YADDA ZA KIYI*

Ki samu ďanyen 'kwai mai yawa sai ki fasa ki buga da kyau sannan ki kawo madarar gari ki zuba a kai sai ki cigaba da juyawa har su haďe jiki, ki samu gwangwamayen alale ki shashafa musu man gyaďa sannan ki dinga ďiban wannan haďin madara da 'kwai kina zuba wa a cikin gwangwamayen, ki ďauko tukunya ki zuba ruwa a ciki sai ki kawo murfi ki kifa a cikin tukunyar (murfin da zai iya shigewa cikin tukunyar ya lullu'be ruwan) sai ki jejjera gwangwamayen a cikin tukunyar ki rufe da faifai ko kuma da murfi, baya daďewa yake dahuwa (baya wuce minti goma) sai ki sauke...😋😋😋 ba sai na baki labarin daďin wannan sweet alale ba idan kinyi zaki bada labari.

Comments

Popular posts from this blog

SHINKAFA DA MIYAR TANKWA

YADDA AKE WAINAR SEMOVITA