SHINKAFA DA MIYAR TANKWA

girkinmu na yau shine shinkafa da miyar tankwa (wato miyar attaruhu da albasa)


                    Kayan hadi
                    Shinkafa
                    Attaruhu
                    Albasa
                    Koren tattasai
                    Kwai
                    Plantain
                    Mangyada


Dafarko uwargida zaki dora ruwa awuta idanyatafasa saiki zuba shinkafa,idantayi rabin dahuwa,saiki sauke kiwanketa kitace kimayar tukunya kisa ruwa kadan yadda zai turarata,ammafa karyayi yawa don ba ason shinkafar tacabe saiki rage wuta.

Saiki dauko attaruhu kiwanke ki jajjaga, saiki albasa itama ayankata yankan tsaye kiwanketa ki barta akwando tasane,sannan kidauko koren tattasai kiyankashi ki ajje agefe, saiki dauko plantain ki bare kiyankata,saiki koma kan shinkafarki idanta turara saiki sauke kibarta a tukunyar tadan sha isaka kafin ki zuba a plaks,saiki dauko kasko ko tukunya kizuba mai kisoya plantain dinnan ki ajje agefe, sannan ki dauko tukunyar dazaki yi miyar ki aciki kizuba mai idan yayi zafi saiki sa albasa idantayi brown saiki zuba attaruhun dakika jajjaga da albasa da koren tattasan saiki juya zaki iyasa farin maggi kadan idankinaso,saiki sa maggi mai star da sauran kalolin maggin da kikeso
kisa seasoning mai dadi saiki zuba citta da kanunfari kadan wanda dama already anaso mace ta dake citta,kanunfari,masoro,gyadar yarabawa mai kamshi da tafurnuwa tadake abinta tazuba aroba idan zaki jar miya ko jallop saikisa, to bayankinzuba saiki juya sosai idan miyar ta soyu saiki rufe kirage wutar kibarshi zuwa minti daya dakinbude zakiga miyar takwanta kayan miyan sunhade jikinsu saiki sauke ki dora ruwa kidafa kwai idan yahuce saiki bareshi kwashe shinkafarki saiki zuba a plet saiki sa miyar agefe kizuba plantain dinma agefe,
sannan kisa kwanki agefe kidanyi musu decoration maikyau shikenan girkinki yakammala saici.

Comments

Popular posts from this blog

SWEET ALALE

YADDA AKE WAINAR SEMOVITA