Posts

YADDA AKE NADA SAMOSA

Image
Kayan Aiki  3 cup Flour 1/4 tsp Salt 1 cup Water 1/2 cup Corn flour MATAKAI 1- Da farko dai zaki zuba duk kayan hadin ki a kwano daya sai ki kwaba kamar soft dough zaki yi shi sai ki murza idan yayi dan ruwa sai kina kara fulawa kina kara murzawa har sai yayi soft fulawar ta bi jikin dough din    2- Zaki murza ki gasa shi kamar yadda zaku gani,dama yadda ake nadin za,a nuna miki    3- Bayan ki gasa shi yayi fadi kamar arebian bread sai ki ninka shi gida biyu yadda zaki gani ki yanka shi    4- Sai ki kara lankwasa shi gida biyu king a ya zama gida hudu ke na   ADAMSY TRADITIONAL MEDICINE WhatsApp/Call or SMS 08051115383, 08093651535 08036066553, 5- Sanna sai ki sami fulawar ki kamar cokali uku ki kwaba ta ruwa ruwa yadda zaki na like bakin samosar ki    6- Sai ki yi nadin kamar bututu(funnel)ki zuba kayan ciki (fillings)   7- Sai ki lankwashe bakin yadda naman ba zai fito ba ki goga ruwan fulawar a bakin karshe ki lankwashe shi    8- Shike nan kin gama nadin samosar ki sai suya ADAMSY T

YADDA AKE WAINAR SEMOVITA

Image
Abuuwa Da Ake Bukata Yeast Sugar Gishiri Albasa Mai Zaki zuba semovita din ki a roba mai dan fadi saikiy mixn dinta da yeast sugar da gishiri kadan saiki kawo ruwan dumi ki kwaba kamar daidai kaurin qullun masa, ki buga qullun sosai, ADAMSY TRADITIONAL MEDICINE WhatsApp/Call or SMS 08051115383, 08093651535 08036066553, Sai ki rufe shi ki barshi ya tashi, idan ya tashi saiki yanka albasa ki buga qullun sosai ya hade jikin sa, saiki soya a abun soya masa, shikenan.

SHINKAFA DA MIYAR TANKWA

Image
girkinmu na yau shine shinkafa da miyar tankwa (wato miyar attaruhu da albasa)                     Kayan hadi                      Shinkafa                     Attaruhu                     Albasa                     Koren tattasai                     Kwai                     Plantain                     Mangyada Dafarko uwargida   zaki dora ruwa awuta idanyatafasa saiki zuba shinkafa,idantayi rabin dahuwa,saiki sauke kiwanketa kitace kimayar tukunya kisa ruwa kadan yadda zai turarata,ammafa karyayi yawa don ba ason shinkafar tacabe saiki rage wuta. Saiki dauko attaruhu kiwanke ki jajjaga, saiki albasa itama ayankata yankan tsaye kiwanketa ki barta akwando tasane,sannan kidauko koren tattasai kiyankashi ki ajje agefe, saiki dauko plantain ki bare kiyankata,saiki koma kan shinkafarki idanta turara saiki sauke kibarta a tukunyar tadan sha isaka kafin ki zuba a plaks,saiki dauko kasko ko tukunya kizuba mai kisoya plantain dinnan ki ajje agefe, sannan ki dauko tukunyar dazaki y

SWEET ALALE

Image
SWEET ALALE * 🥛🥛🍳🍳 * KAYAN HADI * 'Kwai Madara * YADDA ZA KIYI * Ki samu ďanyen 'kwai mai yawa sai ki fasa ki buga da kyau sannan ki kawo madarar gari ki zuba a kai sai ki cigaba da juyawa har su haďe jiki, ki samu gwangwamayen alale ki shashafa musu man gyaďa sannan ki dinga ďiban wannan haďin madara da 'kwai kina zuba wa a cikin gwangwamayen, ki ďauko tukunya ki zuba ruwa a ciki sai ki kawo murfi ki kifa a cikin tukunyar (murfin da zai iya shigewa cikin tukunyar ya lullu'be ruwan) sai ki jejjera gwangwamayen a cikin tukunyar ki rufe da faifai ko kuma da murfi, baya daďewa yake dahuwa (baya wuce minti goma) sai ki sauke...😋😋😋 ba sai na baki labarin daďin wannan sweet alale ba idan kinyi zaki bada labari.

JOLLOF DIN DASHISHI

Image
_*Ingredients*_ _Alkama_ _Attarugu_ _Albasa_ _Maggi_ _Gishiri_ _Curry_ _Mai_ _Carrot_ _Cabbage_ _*METHOD*_ _Zaki gyara alkamar ki, ki wanke ta ki rege saboda tsakuwa ko qasa, zaki bada a 6arza maki ita, manya 6arji ko qanana duk dai wanda kikafi so, bayan an kawo maki saiki wanke wannan 6arjin alkaman naki saiki daura tukunya da madanbaci akan wuta, saiki zuba wannan alkamar taki acikin madanbacin ki rufe sosae yadda zata turaru sosae, zaki bata kamar 20mnts saiki sauke ki wanke, bayan kin wanke saiki dauko attarugunki wanda kin riga kin jajjaga shi tare da albasar da kika yanka saiki sanya acikin wannan dashishin naki da kika wanke, saiki sanya gishiri da duk kalar maggin da kikeso da curry saiki sanya carrot dinki wanki kin riga kin yanka shi tare da cabbage dinki saiki maida dashishin naki akan wuta bayan kin gama hada komai da komai saiki barshi ya cigaba da dahuwa ki bashi kamar 30mnts zuwa 40 don ya dahu sosae saiki sauke ki samu waje mai fadi sosae ki juyeshi aciki s

FRIED RICE

Image
Ingredients: * Shinkafa * Nama * Hanta ko koda * Green peas * Green pepper * Carrot * Cabbage * Peas * Albasa * Attarugu * Maggi * Gishiri * Curry * Mai Preparation: Ki yanka kayan lambunki kanana, ki tafasa namarki da hantarki ki yanka kanana, ki tafasa ruwa,  ki wanke shinkafarki ki zuba, idan shinkafar ta fara alamar dahuwa, da garas-garas din ta sai ki sauke, ki tace, ki dora man ki a wuta, idan yayi zafi za ki yanka kayan lambunki dama kin yanka albasa slice, da attarugu kanana duka sai ki zuba, ki yi ta juyawa, idan suka fara laushi sai ki zuba shinkafarki, da nama da maggi da gishiri da curry, ki yi ta juyawa har sai shinkafar ta karasa dahuwa duk tare da kayan lambun, idan tayi za ki ga ta yi wara-wara ta yi kyau a fuska, kayan lambun kuma zai fito a ciki ya yi shar-shar.